Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 155 Akwai Haske Yanzu Cikin Zuciyata Lyrics
1
Akwai haske yanzu cikin zuciyata
Tun Yesu ya zo wurina.
Aka gafarta mini duk zunubina
Tun Yesu ya zo wurina.
KORUS
Tun Yesu ya zo wurina,
Tun Yesu ya zo wurina,
Ina da kwanciyar rai,
Har da murna sosai,
Tun Yesu ya zo wurina.
2
Yanzu dai na ke da tabbataccen bege,
Tun Yesu ya zo wurina.
Wata rana zan zauna tare da shi can,
Tun Yesu ya zo wurina.
KORUS
3
Ɗanuwa, kana so ka yi murna kuma?
Bar Yesu ya cece ka yau.
Za ya gafarta maka duk zunubanka.
Bar Yesu ya cece ka yau.
KORUS NA ƘARSHE
Bar Yesu ya cece ka yau,
Bar Yesu ya cece ka yau,
Za ka yi kwanciyar rai,
Har da murna sosai,
In Yesu ya cece ka yau.