Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 154 Yesu Yana So Ya Zauna Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 154 Yesu Yana So Ya Zauna Lyrics

 

1
Yesu yana so ya zauna
Cikin zuciyar mutane.
Shi ya ɗauke laifofinka
Ranka kuma ya ke so.

KORUS
Yesu yana bakin ƙofa,
Sai ka ji maganarsa,
Buɗe ƙofar zuciyarka
Yi wa Yesu maraba.

2
Akwai dama domin wasa
Akwai damar aiki kuwa.
Babu wuri domin Yesu
Cikin zuciyar mutane.
Korus

3
Yau ne lokacin alheri,
Akwai ceto dominmu.
Kila gobe babu dama,
Gobe fa ba tamu ba.
Korus

4
Kwanakinmu kamar iska
Suna wucewa da sauri.
Sai ka tuba, karƃi Yesu
Kamin ranar fushinsa.
Korus

Exit mobile version