Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 153 Ga Ƙofa Nan, Buɗaɗɗiya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 153 Ga Ƙofa Nan, Buɗaɗɗiya Lyrics

 

1
Ga ƙofa nan, buɗaɗɗiya,
Mai Ceto ne ya buɗe.
Dukan mai so ya sami rai
Ya bi ta wannan ƙofa.

KORUS
Ga ƙofa dai buɗaɗɗiya
Mai Cetonmu ya buɗe ta.
Ku zo, mu je,
Ku zo ku shiga dai.

2
Ga ƙofa nan a buɗe dai
Kowa ya iya shiga
Mawadaci da talaka
Na kowace kabila.
Korus

3
Ku matso zuwa ƙofan nan,
Yanzu ne loton jinƙai.
Ku karƃi rawani na rai.
Kyauta ce wannan duka.
Korus

4
Mai Cetonmu ya mutu dai
Domin ƴan Adam duka.
Ya buɗe ƙofar samun rai,
Dukan mai so zai samu.
Korus

Exit mobile version