Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 152 Zo Wurin Yesu, Kada Ku Ƙi Lyrics
1
Zo wurin Yesu, kada ku ƙi,
Yesu ke nemanmu duka mu bi.
Kada ku tsaya, yau sai ku ji,
Yesu ke kiranku.
KORUS
Murna, murna, murna za mu yi,
Masu zuwa, Yesu ba ya ƙi.
Can za mu taru tare da shi,
Can cikin mulkinsa.
2
Yara, in ji shi, su na ke so,
Duk ƙanƙanana ku bar su su zo,
Kada ku hana wanda ya so,
Amma ku karƃe su.
Korus
3
Yesu ne hanya, Yesu ne rai,
Makiyayi mai aminci ne dai.
Shi za ya bi da nasa sosai
Har zuwa gidansa.
Korus