Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 151 Yesu Yana Bakin Ƙofa Lyrics
1
Yesu yana bakin ƙofa,
Yana ta da murya,
Ku ƴan Adam duk, ku ji ni,
Shiga ƙofar hanyata.
2
Ƙofan nan da wuyar shiga
Hanya kuwa ƙunƙunta ce,
Masu shiga babu yawa,
Sai mutane kima ne.
3
Dukan masu son adalci,
Dukan masu ƃacin rai,
Masu ladabi a ruhu,
Su ke shiga, su kaɗai.
4
Ba da dukiya za mu je ba,
Ba kuwa da aniya ba,
Ba don aikin nagarta ba,
Sai da bangaskiya kaɗai.
5
Wata ƙofa tana nan kuwa,
Masu shiga sun yi yawa,
Hanyan nan kuwa ke da fādi
Za ta kai su halaka.
6
Hanyan nan da sauƙi ta ke,
Gama babu kokawa
Da jaraba ko mugunta,
Ba kuwa masu hanawa.
7
Ba su ganin inda za su,
Ba tsammanin halaka.
Duniya duk da ruɗin Shaiɗan
Su kan rufe idonsu.
8
Tashi, masu laifi duka,
Sai ku nemi gafara,
Sai ku karƃi kyautar Allah
Sai ku riƙa yin godiya.