Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 150 Ya Mutanen Ƙasan Nan, Musulmi da Ama Duk Lyrics
1
Ya mutanen ƙasan nan, Musulmi da ama duk,
Sai ku kasa kunnenku ga labarin cetonku.
KORUS
Yesu shi ne Mai Ceto wanda Allah ya aiko
Domin fansar ƴan Adam daga bautar zunubi.
2
Babu wani masoyi ko kuwa mai jin tausayi.
Sai dai Yesu haifaffe, shi kaɗai Ɗan Allah ne.
Korus
3
Jinin ransa ne ya bayar domin ceton duniya.
Shi ya ɗauke zunubai, shi ya buɗe ƙofar rai.
Korus
4
Sheƙa gunsa kuwa yanzu, ga shi yana jiranku.
Tuba daga laifinku, nemi ceto wurinsa.
Korus