Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 15 Ya Ubanmu, Ka Bishe Mu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 15 Ya Ubanmu, Ka Bishe Mu Lyrics

 

1
Ya Ubanmu, ka bishe mu
Cikin wannan duniya.
Kai kaɗai mai taimakonmu,
Dube mu da ƙaunarka.
Ba abin da za mu rasa,
In ka zama jigonmu.

2
Ya Mai Ceto, ka yi jinƙai.
Ka san kumamancinmu,
Kai ka sha wahalar giciye,
Domin fansar dukanmu.
Za mu jure har matuƙa
In ka sa albarkarka.

3
Sauko nan, ya Ruhun Allah.
Cika mu da ikonka.
Ba mu ƙauna da salama,
Murna marar iyaka.
Haka za mu ratsa duniya,
Har mu isa gidanka.

Exit mobile version