Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 149 Ya Ku Zukatan Mutane Lyrics
1
Ya ku zukatan mutane,
Rashin sani kuka yi,
Kamar ƃatattun tumaki,
Wurin kiwo ku ke ki.
2
Ko kun san wani kamarsa?
Almasihu ya fi duk
Ƙauna, taimako, har kuma
Ceto daga zunubi.
3
Ya ku zukatan mutane,
Shakka ce ta hana ku?
Sai ku dogara gare shi
Wanda ya ke ƙaunarmu.
4
Sai ku zo, ku ji, ku gwada,
Yesu mai aminci ne.
Maimakonmu shi ya cika
Nufin Ubanmu daidai.
5
Cikin Yesu mu ke samun
Sanin Allah, sanin rai.
Kuma aka ɗora masa
Duk alhakin zunubai.
6
Da kun gaskata maganar,
Da ya sake halinku,
Da ya sabonta zukata,
Da ya zauna cikinku.
7
Ƴanuwa, mu yi godiya,
Sai mu ƙaunace shi dai.
Ba dalilin tsoro kuma
Har iyakar zamanai.