Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 148 Wanda Ya Ke Neman Ceto Daga Zunubi Lyrics
1
Wanda ya ke neman ceto daga zunubi, Wanda ya ke so ya daina nufin zunubi,
Ya zo ya ji labarin wani, shi Mai Cetonmu
Sunansa Yesu ne.
KORUS
Yesu, Yesu ne Mai Ceto,
Yesu, Yesu ne Mai Ceto,
Yesu, Yesu ne Mai Ceto.
Yesu, Mai Ceto ne.
2
Ko ka yi ƙoƙari kome yawan famanka,
Ba ka iya kome don ka ceci ranka ba.
Mai Ceto guda ɗaya ne, tausayi gare shi kuwa,
Sunansa Yesu ne.
Korus
3
Zo, ka kasa kunne ga jawabina yanzu,
Sai ka nemi ceto wurin Ubangijinmu,
Bari neman kowa sai Mai Cetonmu kaɗai, Sunansa Yesu ne.
Korus
