Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 145 Cikin Raina Ga Wahala, Hutu Na Ke So Lyrics
1
Cikin raina ga wahala, hutu na ke so,
Yesu shi kaɗai ya iya taimako.
2
Yana kira, yan kira, yana nemana.
“Zo gare ni, za ka sami hutawa.”
3
“Ka gaji da aikin Shaiɗan? Bautarsa da wuya
Zo gare ni, dukan fansa ni na biya.”
4
“Cikin zuciya ko da sauran shakka har wa yau?
Duba, jinina na bayar, sai ka zo.”
5
“Wanda ya ke zuwa gare ni, ba na korarsa,
Har da kowane mai neman gafara.”
6
Yesu, ina so in bi ka, zama bawanka.
Kai ne yau har muddar raina Sarkina.
