Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 144 Allah. Ya Ba Mu Hasken Rai Domin Mu Haskaka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 144 Allah. Ya Ba Mu Hasken Rai Domin Mu Haskaka Lyrics

 

1
Allah. ya ba mu hasken rai domin mu haskaka,
Jama’a duk su gaskata Yesu Ɗan Allah ne.

2
Shi kuwa ya nuna ƙaunarsa a cikin hasken nan.
Ya aiko Ɗansa, tilo ne, Ya sauko duniyan nan.

3
Wanda ya ƙyale hasken nan, ya fi son duhunsa.
Ba zai ga fuskar Allah ba sai cikin fushinsa.

4
Yanzu ku tuba, bi shi dai, domin ku sami rai.
Ba wata hanyar ceto fa, sai Yesu shi kaɗai.

5
Ya Yesu, ba mu ikonka mu furta ƙaunarka,
Mu shaida. kai ne cetonmu da ƙarfin zuciya.

Exit mobile version