Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 143 In Za Ka Bi Mai Cetonmu Lyrics
1
In za ka bi Mai Cetonmu,
Lura da wannan tun yanzu,
Ba za ya karƃi kome ba,
In ba ka ba shi ranka ba.
2
Aikinka kawai ba ya so,
Ba ya bukatar taimako.
In ba ka ƙaunace shi ba,
Aikinka ba zai karƃa ba.
3
Kayanka kuma ba ya so,
Ba domin kaya ba ya zo.
In ba ka ba shi ranka ba,
Kayanka ba zai karƃa ba.
4
Gama ya bar gidansa can,
Ya ba da jininsa a nan,
Garin ya sayi zuciyarka.
Bar shi ya karƃi mulkinta.
