Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 142 Jinin Yesu Mai Daraja Yana Zubowa Lyrics
1
Jinin Yesu mai daraja yana zubowa
Domin fansar duk jama’a, domina.
KORUS
Jinin Yesu mai daraja za ya tsarkake
Wanda za ya zo ya karƃa, kyauta ce.
2
Ko da zunubanku sun yi kamar mulufi,
Cikin jinin Almasihu za su fita.
Korus
3
Ba abin da za mu biya, duk ya ƙarasa
Yesu yana miƙa mana gafara.
Korus
4
Cikin wuri mafi tsarki sai mu shiga fa,
Don ta wurin jinin Yesu mun tsarkaka.
Korus
5
Kome kokawa da Shaiɗan, akwai nasara.
Gama cikin jinin Yesu iko ‘na nan.
Korus
6
Ran da za mu shiga Sama, sai da jinin nan,
Za mu yabi sunan Yesu ranan nan.
Korus