Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 140 Zamanin Dā, Almasihu Ɗan Allah Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 140 Zamanin Dā, Almasihu Ɗan Allah Lyrics

 

1
Zamanin dā, Almasihu Ɗan Allah
Ya ji tausayinmu, mu ƃatattu.
Shi ma ya rabu da gidan Ubansa
Ya shigo duniyan nan tare da mu.

KORUS
Zuwan Mai Ceto ƙauna ta sa shi,
Allah ya bayar don duniya duk,
Kada su ƃata, sai dai su sami
Ceto da rai kuwa na har abada.

2
Zaman Mai Ceto a wurin mutane
Da yawan so da alheri ya ke.
Kowa ya nema ya gamu da Yesu.
Ya dai same shi mai taimako ne.
Korus

3
Zaman nan nasa na aikin alheri,
Ba shi da aibi, mai ƙauna ne shi.
Ransa ya bayar don fansar mutane,
Allah ya karƃa, mai tsarki ne shi.
Korus

4
Domin zunubinmu Yesu ya mutu,
Bayan ya mutu ma sai binnewa.
Shi ma ya tashi a rana ta uku
Kāna ya hau Sama wurin Uba.
Korus

5
Yesu Mai Cetonmu zai sake zuwa,
Haka alkawari wanda ya yi.
Sa zuciyarmu dai kowace rana,
Bari ya iske mun shirya sosai.
Korus

Exit mobile version