Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 138 Labarin Gafara Da Daɗin Ji Ya Ke Lyrics
1
Labarin gafara da daɗin ji ya ke.
Shi mu ke bayarwa, jawabin Allah ne.
KORUS
Yabonka ne, ya Allah, wannan ya kamata
Jama’a su yi maka don gafara.
2
Alherin gafara an shirya shi sosai,
Da damar samuwa a wurin duk mai rai.
Korus
3
Dalilin gafara, Ɗan Allah aikakke,
Azabarmu ya sha a jikin gungume.
Korus
