Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 137 In Kyautar Allah Ku Ke So Lyrics
1
In ƙyautar Allah ku ke so,
Ku manya duk da yara ma,
Yesu shi ne ya shirya ta,
Yanzu kuwa ta ke samuwa.
KORUS
Yana so ku ku zo
Wurinsa, karƃar gafara
Tun kuna nan a duniya,
Tun shi ma yana samuwa.
Yana so ku ku zo
Wurinsa, karƃar gafara.
2
Ko kuɗi ne bukatarku,
Sutura ma, ko ci, ko sha,
Sai da dalili. Shi ya sa:
“Dalili ya fi dukiya.”
Korus
3
A wajen ceto haka ma,
Tafarkin samu, Yesu ne.
Ko ɗaya ba mai rasawa
A cikin dukan Masu Bi.
Korus
