Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 136 Yesu Ne Mai Ceton Duniya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 136 Yesu Ne Mai Ceton Duniya Lyrics

 

1
Yesu ne Mai Ceton duniya,
Yesu ne Mai Cetonmu.
Shi ya mutu domin dukan
Masu zunubi a nan.

KORUS
Yesu ne Mai Ceton duniya,
Yesu ne Mai Cetonmu.
Shi ya mutu domin duka,
Sa’an nan ya tashi kuwa.

2
Di mun ƃata, ya neme mu,
Tumakinsa ƃatattu,
Shi ya ƙaunace mu duka,
Shi ya kawo mu garkensa.
Korus

3
Mun yi ciwon zunubanmu,
Ya warkad da dukanmu.
Ba ma gani, mun ji tsoro,
Ya fisshe mu lafiya.
Korus

4
Kuma duhu ya dame mu,
Ɓacin zuciya ya zo.
Yesu ne ya kawo haske,
Shi ya kawo kwanciyar rai.
Korus

5
Za ya riƙa kiyaye mu.
Har ya sauko dominmu,
Za ya kai mu can wurinsa,
Nasa ne har abada.
Korus

Exit mobile version