Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 134 Suna Nan, Su Tumaki Tasa’in Da Tara Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 134 Suna Nan, Su Tumaki Tasa’in Da Tara Lyrics

Hymn 134 Suna Nan, Su Tumaki Tasa’in Da Tara Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 134 Suna Nan, Su Tumaki Tasa’in Da Tara Lyrics

 

1
Suna nan, su tumaki tasa’in
Da tara lissafinsu,
Amma ɗaya ta bace a garken nan,
Ta yi nisa da sauransu.
Ita kaɗai, ga dare ya zo,
Can a jeji, ba taimako,
Can a jeji, ba taimako.

2
Ga waɗannan duka sun kwanta nan.
Ko su ba su isa ba?
Mai garke ya amsa, ko kaɗan,
Zan je neman ɗaya ɗin nan.
Can ya tafi da azabar rai,
Can ya iske ta, abin tausayi,
Can ya iske ta, abin tausayi.

3
Amma zafin wahalar da shi ya sha
Ba wanda ya taɓa ji.
Har ya sami abinsa da kyar da rai,
Da jinƙai ya ɗauke ta.
Da ɗari da ciwo ya iske ta can
A bakin mutuwa, tinkiyan nan,
A bakin mutuwa, tinkiyan nan.

4
Ga jini a hanya a sarari,
Ya bi sawun makiyayi.
Ai, ya zubar da shi garin hanzari,
Domin zafin ƙaunarsa.
Ƙaya ta soke shi, jeji ya bi,
Dutse ya buga, ba ganin gari.
Dutse ya buga, ba ganin gari.

5
Alhamdu ga Allah mai runduna,
Alhamdu ga Almasihu.
Mala’iku na Sama sun ɗaukaka shi
Mu ma, muna yin godiya.
Muna yabonsa, ya cece mu,
Mu, muka ƃace, ya komo da mu,
Mu, muka ƃace, ya komo da mu.

Post navigation

Previous: Hymn 116 Ta da Kanku, Ƙyamare, Halleluya Lyrics
Next: Hymn 139 Sai In Ba Ku Labarin Nan, Zance Mai Ba da Rai Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version