Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 131 Ka Zo, Ka Zo Immanuel Lyrics
1
Ka zo, Ka zo Immanuel
Ka fanshi ƴaƴan Isra’ila.
Da ka fashe su daga bauta
Ka shirya musu yankin ƙasa ma
KORUS
Murna! Murna! Yi murna, dukanku !
Ga Allahnku, ya zo ya cece ku.
2
Ka zo, ka zo, Immanuel
Ka kafa sabon Isra’ila
Da muna cikin bautar Shaiɗan,
Amma ka zo, ka tsinke sarƙoƙi
Korus
3
Ka zo, ka zo, Immanuel
Ka tara ƴaƴan Isra’ila
Mu muna zama da shirinmu
Har ran da za ka zo ka ɗauke mu
Korus
Murna! Murna! Yi murna, dukanku !
Ga Allahnku, zai zo ya fyauce mu.