Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 13 Kai Ne Ubanmu, Gare Ka Mun Zo Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 13 Kai Ne Ubanmu, Gare Ka Mun Zo Lyrics

 

1
Kai ne Ubanmu, gare ka mun zo.
Bayinka ƴaƴanka, kai mu ke so.
Karƃi addu’armu yanzu,
Allah Mai Girma, Mahaliccinmu.

2
Kai ne Mai Cetonmu ƙaunatacce.
Pansassu, cetattu, kai mu ke bi.
Karƃi addu’armu yanzu,
Yesu Maɗaukaki, Masoyinmu.

3
Kai ne Aikakke na Uba da Ɗan.
Babu marayu nan gaba daɗai.
Cikinmu yi addu’a yanzu,
Ruhu Mai Tsarki, Mai Taimakonmu

4
Uba, Mai Ceto, Mai Taimako, ɗaya.
Allah, da Kalma, da Ruhunsa, ɗaya.
Duba yanzu sujadarmu,
Karƃe ta, karƃe mu, naka ne mu.

Exit mobile version