Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 127 Wata Rana Za Mu Gan Shi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 127 Wata Rana Za Mu Gan Shi Lyrics

 

1
Wata rana za mu gan shi,
Yesu Ubangijinmu.
Za mu tsaya a gabansa
Wanda ya ke ƙaunarmu.

KORUS
Wata rana za mu gan shi
Cikin dukan daraja.
Za mu yi masa sujada.
Za mu duba fuskarsa.

2
Mu dai ba mu ganin Yesu
Cikin wannan duniya
Amma can a gidan Sama
Za mu duba fuskarsa.
Korus

3
Ran da muka kai gun Yesu,
Shi zai shafe hawaye,
Babu sauran ƃacin zuciya,
Sai dai murna za mu yi.
Korus

4
Za mu gan shi, Halleluya!
Za mu ga Mai Cetonmu.
Za mu faɗi a gabansa
Wanda shi ke Sarkinmu.
Korus

Exit mobile version