Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 125 Yesu Ubangijinmu Yana Gun Uba Yanzu Lyrics
1
Yesu Ubangijinmu yana gun Uba yanzu,
Yana shirya mana wurin zama can.
Wata rana, wata sa’a, za ya dawo duniya,
Za ya fyauce Masu Binsa nandanan.
KORUS
Muna jiran Sarkinmu, muna duban hanyarsa
Ko da rana ya sauko, ko da dare ya iso,
Sai ya iske mu da shirin karbarsa.
2
Kana daɗi za mu ji, za mu ga Ubangiji,
Muna zamanmu tare har abada.
Babu sauran ƃacin rai, farinciki ne kaɗai,
Kullum murna za mu yi, ba fasawa.
Korus
3
Ƴanuwa, ku zo yanzu, Yesu za ya wanke ku,
Za ya kyauta muku rai har abada.
Zo ku bi Mai Cetonku, faɗa masa laifinku,
Shi ya shirya muku gafara tun dā.
Korus