Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 124 Yesu Kristi Yana Zuwa Domin Ya Karƃe Mu Lyrics
1
Yesu Kristi yana zuwa domin ya karƃe mu.
Duk Ekklesiya za ta gan shi, Mai Cetonta ne.
KORUS
Halleluya ga Yesu, ga Yesu Mai Ceto,
Halleluya ga Yesu, Mai Cetonmu ne.
2
Ƙanƙanana duk da manya, Yesu yana sonsu,
Masu sonsa, masu tuba da zuciya ɗaya,
Korus
3
Muna jira, Ubangiji, mu ƴaƴanka duka,
Ko da rana, ko da dare, koyaushe ka zo.
Korus
4
Wata rana, wata sa’a, lalle kana zuwa.
Muna zamanmu da shiri har ran da ka zo.
Korus