Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 122 Wata Rana, Wata Sa’a, Yesu Kristi Za Ya Zo Lyrics
1
Wata rana, wata sa’a, Yesu Kristi za ya zo,
Masu Binsa za su ga darajarsa
Daga kowace kabila, ƙasashe dabam dabam,
Za mu taru wurin Ubangijinmu
KORUS
Za mu taru, za, mu taru,
Za mu taru can a Sama, fansassu da cetattu.
Za mu taru, za mu taru,
Wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.
2
Masu Bi da su ke barci, Yesu za ya kira su,
Za su fito daga cikin kabari,
Cikin Sama za su gan shi, za su zo su tarbe shi,
Za mu taru wurin Ubangijinmu.
Korus
3
Waɗanda suka riga mu zuwa cikin birnin nan
Za mu sake ganinsu a wurin can.
Babu sauran kewa kuma, babu sauran rabuwa,
Za mu taru wurin Ubangijinmu
Korus