Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 120 Duba, Yesu Yana Zuwa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 120 Duba, Yesu Yana Zuwa Lyrics

 

1
Duba, Yesu yana zuwa.
Dā ya mutu dominmu,
Dubban dubbai, tsarkakansa,
Duka za su rako shi.
Halleluya! Halleluya!
Za ya nuna ikonsa.

2
Duk jama’a za ta gan shi,
Su da suka soke shi,
Cikin tsoro za su san shi,
Ba sa so su tarbe shi.
Suna kuka, suna kuka,
Suna duban Sarkinsu.

3
Dā ya zo da kalmar ceto,
Dā ya zo da gafara.
Za ya komo mai shari’a,
Za mu taru gabansa.
Wa zai tsaya, wa zai tsaya
Cikin ranar fushinsa?

4
Shi da kansa za ya sauko,
Ranar fansarmu ta zo,
Za mu tarbe shi a hanya,
Masu rai da matattu.
Cikin Sama, cikin Sama
Za mu ga Ubangiji.

5
Zo da sauri, Almasihu,
Masu Bi ‘na jiranka.
Ƙarfii mulki, ƙarfi yabo,
Naka ne har abada.
Halleluya! Halleluya !
Zo da sauri, zo yanzu.

Exit mobile version