Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 12 Allah Maɗaukaki, Sarki Madauwami Lyrics
1
Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami,
Mu yabe ka.
Kai ne Mahalicci, kai ne mai aminci,
Kai ne mafifici har abada.
2
Mun taru wurinka, kai ne madogara,
Mun yabe ka.
Kai ne mai ƙaunarmu, kai ne mai fansarmu,
Kai ne mai tsaronmu har abada.
3
Bayyana girmanka, nuna darajarka,
Kusance mu.
Tsarkake zukata, sauko da ikonka,
Furta maganarka, ya Allahnmu.
4
Mallaki ƴaƴanka, ƙarfafa bayinka
A duniyan nan.
Yi amfani da mu, kwaƃi ragwancinmu,
Mai da mu nan gaba manzanninka.
