Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 119 Zo, Mutane, Rera Waƙa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 119 Zo, Mutane, Rera Waƙa Lyrics

 

1
Zo, mutane, rera waƙa,
Cika sammai da yabo.
Yabe shi, Mai Magani ne,
Don ya ceci duniya.
Makiyayi, Mai Cetonmu,
Ana biyayya da shi.

2
Saboda cetonmu ne fa,
Ya zo ya ba da jininsa,
Ya yi aikin gafara ma,
Ya mutu, mun huta ma.
Tashinsa na ɗaukaka ne,
Sarkin rai har abada.

3
Yanzu bisa kursiyinsa
Girma, iko nasa ne.
Ana rera, Halleluya,
Waƙar ƴaƴan haske ce,
Shi Sarki nc da Shugaba,
Nasara duk tasa ce.

4
Ga giraya da algaita,
Rera waƙar yabonsa.
Duniya ma ki saurare mu,
Sarkin rai ya rinjaya!
Rago wanda aka kashe
Ya rayu, ya tashi kuwa.

5
Yabo, ɗaukaka ga Uba,
Yabo, ɗaukaka ga Ɗa,
Yabo, ɗaukaka ga Ruhu,
Uku cikin ɗaya ne.
Makaɗaicin Allah namu
Girma, yabo nasa ne.

Exit mobile version