Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 118 Almasihu Yana Nan! Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 118 Almasihu Yana Nan! Lyrics

 

1
Almasihu yana nan!
Tsoron mutuwa ya ƙare.
Wannan muka gaskata,
Ikon kabari banza ne. Halleluya!

2
Almasihu yana nan!
Ƙofar rai shi ne ya buɗe.
Mutuwa fa ƙaura ce
Zuwa rai na har abada. Halleluya!

3
Almasihu yana nan!
Dominmu ne shi ya mutu.
Tsarkin zuciya wajib ne
Ga waɗanda ya fanshe su. Halleluya!

4
Almasihu yana nan!
Ba mai hana mu ƙaunarsa.
Ko da rai ko babu shi,
Mun sa kanmu a hannunsa. Halleluya!

5
Almasihu yana nan!
Mai sarautar dukan duniya.
Sai mu bi ta gurbinsa,
Mu yi mulki cikin Sama. Halleluya!

Exit mobile version