Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 116 Ta da Kanku, Ƙyamare, Halleluya Lyrics
1
Ta da kanku, ƙyamare, Halleluya!
Almasihu na ɗaɗɗe Halleluya!
Yau ya karƃi mulkinsa, Halleluya!
Yau ya hau Samaniya, Halleluya!
2
Aikinsa ya gama dai, Halleluya!
Tsarkakewar mutane, Halleluya!
Bisa kursiyinsa yanzu, Halleluya!
Yana roƙo dominmu, Halleluya!
3
Yesu ba zai bar mu ba, Halleluya!
Yana wurinmu lalle, Halleluya!
Ruhunsa mai taimako, Halleluya!
Yana zaune cikinmu, Halleluya!
4
Yesu za ya komo nan, Halleluya!
In ya shirya wuri can, Halleluya!
Za ya karƃi Masu Bi, Halleluya!
Za mu hau tare da shi, Halleluya!