Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 114 Halleluya! Halleluya! Halleluya! Wahalarka Lyrics
1
Halleluya! Halleluya! Halleluya!
Wahalarka, Mai Fansarmu,
Ta kawo ceto dominmu,
Ta buɗe rijiyar rai yanzu, Halleluya!
2
Aikin Shaiɗan da gurinsa,
Ka ƃata su da giciyenka,
Ka ba da rai domin mu rayu, Halleluya!
3
Kai ne kaɗai mai nasara
Kan Shaiɗan duk da ƴaƴansa,
Ka kā da su da ikonka, Halleluya!
4
Kai ne ka jawo mu wurinka,
Kai ne ka kawo gafara,
Kai ne ka ba mu Ruhunka, Halleluya!
5
Kai ne ka gama cetonmu,
Ka hau can Sama dominmu,
Kai ne mai zuwa dominmu, Halleluya!
6
Yabo ga Allah sai mu yi,
Yabo ga Yesu, Masu Bi,
Yabo ga Ruhu Mai Tsarki, Halleluya!