Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 113 Ya Allah, Miƙa Hannunka, Ka Tsai da Haukansu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 113 Ya Allah, Miƙa Hannunka, Ka Tsai da Haukansu Lyrics

 

1
Ya Allah, miƙa hannunka, ka tsai da haukansu,
An kashe Almasihunka ta hannun miyagu.

2
Ba za ka bar Mai Tsarkinka cikin kabari ba.
Ba za ka bar maƙiyansa su ci nasara ba.

3
Dā, kayayuwa tsinana sun soki goshinsa.
Yanzu ka naɗa Almasihu a hannun damanka.

4
Shi wanda aka kunyata a cikin duniyan nan,
Ka tashe shi da daraja, ka ba shi girma can.

5
Shi ne ya mutu dominmu, ya ɗauki giciyensa.
Mun sami rai da lafiya ta wurin dūkansa.

6
Idan mun mutu tare nan, mun ɗauki giciyensa,
Tare kuwa za mu yi murna a cikin mulkinsa.

7
Ina misalin yabonka, ya Yesu Almasihu?
An sanya mulkin kome nan ƙarƙashin sawunka.

Exit mobile version