Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 112 Can Cikin Kabarin, Yesu Mai Ceto Lyrics
1
Can cikin kabarin, Yesu Mai Ceto
Ya kwana uku ɗin, Ubangiji.
KORUS
Shi aka ɗaukaka.
Aka watse duk maƙiyansa,
Duk mazaunan duhu ba sa tsaronsa,
Yana zuwa da wannan shaidar nasara,
Yana zuwa, yana zuwa,
Halleluya, yana zuwa.
2
An tsare kabarin Yesu Mai Ceto
Banza ne hatimin, Ubangiji.
Korus
3
Ya raina mutuwa, Yesu Mai Ceto,
Ya tsinke sarƙarta, Ubangiji.
Korus