Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 111 Zaƃaƃƃe Na Allah, Shi Lyrics
1
Zaƃaƃƃe na Allah, shi,
Aikakke na ainihi,
Nufin Allah duk ya yi,
Ubangiji Almasihu.
2
Yesu aka kunyata,
“Shi ba wani abu ba,”
Aka ce. Ai, shi ya sa
Aka raina Almasihu.
3
Shi, a jikin gungume,
Ga shi nan kuwa, ɗaurarre!
Aka kashe shi sosai,
Mai alheri ne ya mutu.
4
Mutuncinsa aka ci,
Zub da jini aka yi,
Karƃar ceto aka ƙi.
Jinin Yesu ya fanshe mu.
5
Riƙe shi ba dama fa,
Ko a cikin mutuwa.
Allah ma ya ɗaukaka
Ɗansa, Yesu Almasihu.
6
In ya komo wata ran,
Zai tashe mu daga nan,
Har ya kai mu gun Uban,
Rerawa ma yi wa Yesu