Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 110 Kai Ne Mu Ke Tunawa, Giciyenka da Raɗaɗi Lyrics
1
Kai ne mu ke tunawa, giciyenka da raɗaɗi.
Ga mu nan a durƙushe, Ubangiji Yesunmu.
2
Kabari, O Kabari, kana shafe zunubi,
Ƙaunarsa mai zurfi kuwa, ƙaunar Almasihu ce!
3
Ana duhu loton nan, kana mutuwa tudu can.
Allah ne ya yad da Ɗan, Almasihu Yesu ne.
4
Ba ka cikin matattu, tashinka ya kwance mu.
Mu ne naka fansassu, Ubangiji Yesunmu.
5
Zaman tsaro sai mu yi, kwanaki na ƙarshe ne.
Muna jiran Sarkinmu, Ubangiji Yesu ne.
6
Begenmu mu kai kursiyi tare da Ubangiji,
Marar laifi kowanne, duka ƴaƴan Allah ne.
