Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 11 Maɗaukakin Sarki Madauwami Ne Lyrics
1
Maɗaukakin Sarki madauwami ne,
Kai ne kuma mafarin hikima duk.
Walƙiyar darajarka ta makanta mu,
Mai iko, mai nasara, ya Allahnmu.
2
Mulkinka mai haske ya tabbata nan,
A hankali, a natse saukowarsa.
Albarkarka tana zubowa kanmu,
Alheri mai yawa da nagartarka.
3
Kai ne mai rayad da talikanka duka,
Da lafiya da ƙarfi da iyawa kuwa.
Mun ga jamalinka cikin halitta,
Gwanintar aikinka ka bayyana kuwa.
4
Da rana da wata har taurari kuwa,
Kyawawan tafukka, da Kogin Kwara,
Da duwatsu duk da tuddai suna yi
Wa sunanka yabo, ya Mahalicci.
5
Ya Ubangiji mai girma, Mai Tsarki ne kai; .
Allah ne na zurfafa da al’arshi,
Mala’ikunka suna yin sujada,
Mu fa sai biyayya za mu yi maka.