Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 109 Jama’a Duk, Ku Zo Mu Yi Yabo Ga Allahnmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 109 Jama’a Duk, Ku Zo Mu Yi Yabo Ga Allahnmu Lyrics

 

1
Jama’a duk, ku zo mu yi yabo ga Allahnmu.
Mu gode domin Yesunmu ya ɗauke laifinmu.

2
Shari’armu mutuwa ce, Yesu ya ɗauke duk.
Ya ba da ransa dominmu, domin ya fanshe mu.

3
An kafa shi da ƙusoshi a bisa giciye,
Ba domin laifofinsa ba, amma don namu ne.

4
Yanzu ko ranar mutuwa, ba zan ji tsoro ba.
Yesu ya ɗauke laifina, ba zai kāshe ni ba.

Exit mobile version