Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 108 Zo Wurin Giciyen Yesu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 108 Zo Wurin Giciyen Yesu Lyrics

 

1
Zo wurin giciyen Yesu, ku masu ƃacin rai,
Ku masu nauyin kaya, zo wurin giciyensa.
Ba wata hanyar ceto, ba wani taimako,
Yesu kaɗai ya mutu domin ya cece mu.

KORUS
Zo wurin giciyen Yesu, saukad da kayanku,
Yesu ya ba da ransa domin ya cece mu.

2
Zo wurin giciyen Yesu, ku masu zunubi.
Wanda ya kasa tashi, Yesu ya kira shi.
Kowane kayan laifi wanda ke danne ku,
Dukan kurakuranku, Yesu zai ɗauke su .
Korus

3
Zo wurin giciyen Yesu, ku masu neman rai.
Mutuwa ta bi kan kowa, rai kyautar Allah ne.
Duba Mai Ceton duniya can bisa itace,
Wanda ya ba da gaskiya, shi dai zai sami rai.
Korus

Exit mobile version