Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 107 Ran da Na Ga Mai Cetona Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 107 Ran da Na Ga Mai Cetona Lyrics

 

1
Ran da na ga Mai Cetona
A Kabari kan giciye,
Na ga ƙaunar Ubangijina,
Na ba shi dukan zuciyata.

2
Ya mutu dai don laifina,
Wahalata shi ne ya sha,
Wane ni fa har da zan ƙi
In karƃi kyautar cetonsa?

3
Ga jininsa ya bayar dai,
Ga raɗaɗinsa domina.
Ya Ubangiji, karƃe ni,
Ka yafe mini laifina.

4
Na gode maka, ya Yesu,
Don dukan aikin cetona,
Na ba ka rai da zuciya duk,
Ni naka ne har abada.

Exit mobile version