Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 106 Me Za Mu Ce da Yesu? Ɗan Ragon Allah Ne Lyrics
1
Me za mu ce da Yesu? Ɗan Ragon Allah ne.
Mai ɗauke kayan zunubi na duk jama’a ne.
Ka ba ni wannan sani, azabar da ka sha.
Mai Gaskiya, Mai Tsarki, ka ɗauke laifina
2
A cikin sa’ar mutuwa Mai Cetonmu ya ce,
“Uba, yi musu gafara, sun yi a jahilce.”
Ka ba ni wannan sani, alherin da ya sa
Maɗaukaki, Mai Tsarki, ya ɗauke laifina.
3
Rana ta rufu sarai, duniya ta duhunta,
A Sama duk mala’iku sun kasa dubawa.
Ka koya mana sanin wannan asirinka,
Dalilin da Mai Tsarki ya ɗauke laifina.
4
Azaba duk ta wuce, Mai Nasara ya ci.
A hannun daman Allah ne ya tsaya, Maɗaukaki.
Ka koya mana sanin iko na tashinka,
Mai Tsarki, Mai Nasara, Yesu Mai Cetona.