Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 104 Duba Dai Mai Fansarmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 104 Duba Dai Mai Fansarmu Lyrics

 

1
Duba dai Mai Fansarmu
Ɗauke da zunubanmu,
Yana shan wahalarmu,
Halleluya, Mai Cetonmu !

2
Raini, duka, nasa ne,
Ba’a, kunya, giciye,
Mutuwa rabonsa ne,
Halleluya, Mai Cetonmu!

3
Ba ya yi zilama ba,
Ba ya faɗi ƙarya ba,
Ba ya yi alfarma ba,
Halleluya, Mai Cetonmu!

4
Ba ya buɗe baki ba,
Ba ya yi kashedi ba,
Ba ya mai da zagi ba,
Halleluya, Mai Cetonmu!

5
Ga shi bisa itace,
“Gafarta musu,” ya ce,
Duba ceto cikakke,
Halleluya, Mai Cetonmu!

Exit mobile version