Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 102 Yesu Kristi, Mai Cetona Lyrics
1
Yesu Kristi, Mai Cetona
Ɗan Allah Mai Tsarki ne.
Halleluya, halleluya.
2
Ina shaidar suna naka,
Sunanka mai daraja.
Halleluya, halleluya.
3
Ina girmama sunanka,
Ubangiji Mai Ceto. Halleluya, halleluya.
4
Jinin Yesu ne ya zama
Fansar masu zunubi.
Halleluya, halleluya.
5
Ina ɗaukaka sunanka,
Yesu, kai mai ba da rai.
Halleluya, halleluya.
6
I, zan shaida sunan Yesu
Har ma duniya duk ta ji.
Halleluya, halleluya.
7
Allah ya yi ƙaunar duniya,
Ƙaunarsa mai girma kuwa.
Halleluya, halleluya.
8
Ni na gaskata da Yesu
Ɗan Allah Mai Tsarki ne.
Halleluya, halleluya.