Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 101 Suna Mai Daɗi Yesu Ne A Kunnen Masu Bi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 101 Suna Mai Daɗi Yesu Ne A Kunnen Masu Bi Lyrics

 

1
Suna mai daɗi Yesu ne a kunnen Masu Bi.
Alhini, tsoro, ƃacin rai, korarsu duk zai yi.

2
Yana ƙarfafa zuciya ta masu ciwon rai.
Manna ne shi ga Masu Bi, ga dukanmu, jinƙai

3
I, sunan Yesu ceto ne, shi ne maƃoyina,
Ƙarfina, pana, garkuwata, begen bangaskiyata.

4
Yanzu a cikin duniya, na kasa yabonka,
Shaidata duk da aikina sai dai da ikonka.

5
Amma a wurin zamanka, zan duba fuskarka.
Waƙa zan yi mai daɗin ji, yabo ga sunanka.

Exit mobile version