Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 100 Dogara Da Sunan Yesu Lyrics
1
Dogara ga sunan Yesu
Ta kan sa a sami rai.
Gama ba ceto ga wani
Ba kuwa hanya sai dai shi.
KORUS
Yesu, Yesu, ina son ka,
Kai kaɗai Mai Ceto ne.
Yesu, Yesu, ni zan bi ka
Daga nan har abada.
2
Jinin Yesu ya fanshe ni.
Yana shafe zunubai.
Na jingina wurin Yesu.
Ya karƃe ni bawansa.
Korus