Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 10 Muna Son Wurin Nan Na Darajar Allah Lyrics
1
Muna son wurin nan na darajar Allah.
Murna ta ɗakin na ta fi a kwatanta.
2
Ɗakin addu’a ne na taron bayinka.
Lalle fa kana nan tare da jama’a.
3
Wurin Baftisma fa mu ke sonsa ƙwarai,
Gama nan Ruhunka ke ba da alherai.
4
Muna son Tebur ma, wuri ƙaunatacce.
Nan ka ke ciyad da mu cikin bangaskiya.
5
Maganarka ta rai, ita ma mu ke so.
Ta ba da kwanciyar rai, salama ta kan kawo.
6
Yanzu mu ke ta yin waƙa ta jinƙanka,
Amma can Sama fa da waƙar nasara.
7
Ya Yesu, ƙara dai alheri da ƙauna
Ga mu jama’arka, mu dinga sujada.