Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 1 Ubangiji Allah, Ga Mu Nan Gabanka Lyrics
1
Ubangiji Allah, ga mu nan gabanka.
Tun da farin hasken safe, mu ke nemanka.
Muna yabon sunanka, ya Mai Iko Duka,
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
2
Ubangiji Uba, kai ne farkon kome,
Kai ka ba da Ɗanka Yesu domin cetonmu.
Mu da muka tayar, kai ka ji tausayinmu.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
3
Ubangiji Yesu, kai ne Almasihu,
Kai ka fanshi bayin Shaiɗan daga bautarsa.
Kai ka ba da jininka domin mu mutane.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
4
Ubangiji Ruhu, sunanka Mai Tsarki,
Kai ne kana koya mana hanyar cetonmu.
Kai ne jagabanmu, kullum sai mu bi ka.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
5
Allah Ubangijinmu, ɗaya cikin uku,
Harshe ba ya iya faɗin girman sunanka.
Uba, Ɗa, da Ruhu, uku cikin ɗaya,
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
