Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 574 Yesu Kristi, Muna Jira Lyrics
1
Yesu Kristi, muna jira
Alkawalin Allahnmu.
Annabawa suna shaida
Kana batun cewarsu
Za ta yi ciki budurwa
Ikon Ruhun Allah ne
Zo da sauri, albarka mu
Cika duka annabci
2
Baitalahmi, ƙauyen Dauda
Cikin Yahudiya ne.
Shi ne wurin haifuwarka
Yadda Mika ya faɗi.
Issufu da Maryamu
Sun yi bulaguro can
Saboda lissafin ƙasa
Domin dokar Romawa.
3
Yesu, kana da sunaye
Kirgarsu, su nawa ne?
Almasihu da Shafaffe
Sarkin salama kai ne.
Begen duniya, Immanuel
Mashawarci mai kyau ne.
Kalmar Allah, Hasken haske
Mai farko da Mai ƙarshe.