Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 602 Zunubi Baƙi Kirin Lyrics
1
Zunubi baƙi kirin
Ya ƃata halina,
Amma da jinin Yesu
An wanke zuciyata.
An mai da ita fara.
An sake halina.
Zan tafi wurin Yesu
Gida mai daraja.
2
Kai fa ba za ka zo ba?
Ka nemi gafara
Ta wurin jinin Yesu,
A wanke zuciyarka,
A mai da ita fara,
A sake halinka,
Ka tafi wurin Yesu,
Gida mai daraja.