Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 352 Addu’a Babu Fasawa Lyrics
1
Yesun mu kafin ya tafi sama
Ya yi mana umurni cewa
Ku yi addu’a ba fasawa
Domin mu sami nufinsa
KORUS
Ku yi addu’a ba fasawa
Domin kada ku faɗa jaraba
Ruhu ya yarda jiki rarauna
Ku yi magana da Allah.
2
Akwai wahala cikin duniya
Wadda babu misalinta
Ku yi addu’a babu fasawa
Domin nassara da duniya.
Korus
3
Akwai jaraba cikin duniya
Wadda babu misalinta
Ku yi addu’a babu fasawa
Kada ku faɗa jaraba.
Korus
4
Ya Yesu Almasihu
Lokacin da nike addu’a
Ka ji ka amsa addu’ata
Domin in aika nufinka.
Korus