Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 368 Allah Ya Ƙamnace Mu, Duk Ƴan Duniya Lyrics
1
Allah ya ƙamnace mu, duk ƴan duniya
Ya aiko mana Yesu, ɗansa, tilonsa
Yesu ya bada ransa har ga mutuwa
Don ya ba mu gafara.
2
Yesu ya kwana uku cikin kabari
Ya tashi don ya ba mu rai madawami.
Ya sake hawa sama gun Maɗaukaki,
Za ya zo ya karɓe ni.