Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 221 Almasihu, Pa Babba, Kai Ne Dutsen Cetonmu Lyrics
1
Almasihu, pa babba, kai ne dutsen cetonmu.
Sa mu cikin inuwarka, bar mu shiga kariyarka.
Duk mun kasa adalci, duk mun aika zunubi,
Kai madogararmu ne, kai dai matserarmu ne.
2
Ko mun kawo sadaka, ko mun daina ratsewa,
Dukan namu ƙoƙari ba ya iya cetonmu.
Kai kaɗai matsakanci, aikin sulhu naka ne.
Mutuwarka da tashinka su sun kawo gafara.
3
Ga mu nan gun giciyenka, muna jiran ikonka.
Kau da dukan zunubi, rashin ƙwazon Masu Bi.
Da jini mai daraja, wanke mana zukata. Tsarkake mu duk yanzu don mu cika nufinka.
4
Ya maƃuyar tsarkaka, nuna ƙarfin cetonka.
Ba mu ikon nasara, tsai da ikon magauta,
Kwaƃi duk muguntarsu, rushe duk dabarbaru.
Sai ka taya mu yanzu, ƙarfafa rayukanmu.